10 Nuwamba 2020 - 13:07
Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Sanar Da Kwato Yankuna Da Dama A Yankin Nogorno-Karrabah

Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Sanar Da Kwato Yankuna Da Dama A Yankin Nogorno-Karrabah

ABNA24 : Shugaban kasar ta Azerbaijan Ilham Aliyev ya sanar a yau Litinin cewa; Sojojin kasarsa sun yi nasarar shimfida ikonsu akan yankuna da dama da suke yankin Karrabah.

Aliyev ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Sojoji sun yi nasarar ‘yanto da garuruwan Gubo, Dilagagarda da Yal Bir Hamidali. Sai kuma garuruwan Yukahri da Yaglifand da Dilagard da Sayyid Mahmudlo.

Bugu da kari wasu garuruwan da shugaban na kasar Azerbaijan ya sanar da cewa sun ‘yanto da su daga mamayar Armenia, sun kunshi: Aliskirly, Kojalisky da Sosanling da kuma Domy.

Tun a ranar 27 ga watan Satumba ne dai fada ya barke a tsakanin sojojin kasashen Azerbaijan da kuma Armenia.

Tare da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a tsakanin kasashen biyu, sai dai daga lokaci zuwa lokaci ana samun keta yarjejeniyar daga dukkanin bangarorin biyu.

342/